[Labari] An Bude Sabuwar Cibiyar Kasuwancin Cinikayyar Ayyukan Noma Da Kiwo

Bude Cibiyar Kasuwancin Cinikayyar Ayyukan Noma Da Kiwo a Yanar Gizo

A safiyar wannan rana ta talata 01 january 2019 muke sanar da al’umma bude cibiyar kasuwancin Ayyukan Noma Da Kiwo,
Muna gabatar muku da sabuwar cibiyar cinikayyar ayyukan da suka shafi noma da kiwo a Nigeria wacce aka yi mata suna da Agribusiness Technology (changing the face of Agriculture)
Wannan cibiya an samar da ita ne ga dukkan masu sha’awar sana’ar noma da kiwo domin samun cigaba a sana’oin su na yau da kullum a wannan saha ta yanar gizo-gizo, cibiyar ta Agribusiness Technology ta samar da wani kasaitaccen (website) na musamman domin tunkarar tarin kalubalen dake fuskantar tafiyar aikin noma da kiwo a wannan saha.

Nasan dai dukkannin masu gudanar da ayyukan noma ko kiwo na da masaniya kan kalubalen dake fuskantar mafiya yawan masu wannan sana’a, ba don komai ba sai don rashin samun cigaban ilimin zamanin dake da alaka da ayyukan na noma da kiwo, hakan ya sanya wasu suke samun asara mai yawa a yayin gudanar da ayyukan nasu, wasu kuma suke rike da amfanin gonar da suka noma a wajen su ba tare da sun siyar dashi ga masu bukata ba, saboda magance wadannan tarun matsaloli hakan ya sanya samarwa da wannan cibiya ta (Agribusiness Technology) dandali (website) a yanar gizo-gizo domin taso tafiyar a gaba, ba don komai ba sai don ganin an wayarwa da masu wannan sana’a kai gami da tallata hajar su domin samun riba mai kyau a kankanin lokaci.

Shin ko wane (website) cibiyar ta Agribusiness Technology ta samar?

Dalilin wannan matsalolin ya sanya cibiyar samar da inda zata wayarwa da al’umma kai, da kuma basu damar tallatawa mabukata hajojin su domin musayar amfanin noma da kiwo ga al’ummar da suke da bukata ta hanyar www.agritech.com.ng

Daya daga cikin jagororin cibiyar yayi karin haske akai kamar haka:

“Toh! Alhamdulillah, duba da halin da masu harkar noma da kiwo ke ciki hakan yasa muka yi karamin yunkuri inda muka samar da wannan cibiya wacce muke sa ran zata taimaka wajen dakile kalubalen da masu noma da kiwo ke fuskanta, sannan zamu yi amfani da shafin (website) wajen bayyanawa duniya halin da ayyukan noma da kiwo suke ciki anan Nigeria, wannan dandali na www.agritech.com.ng zai mayar da hankali wajen wadancan abubuwa, A gefe guda kuma akwai bangarori wanda a turance ake kira da
•Agricultural Supplies
• Animal Supply
• Mechanized Agriculture
• Aquaculture
• Livestock & Poultry
Duba da yadda aka yi nisa wajen kwarewa a shafukan yanar gizo-gizo hakan ya sanya muka yi amfani da hanyoyin da zamu saukakawa al’umma amfani da website dinmu kamar haka:
1. Akwai “Translator” da zaka iya canja shafin zuwa yaren da kake bukata,
2. Zaka iya yin searching na wani abu da kake nema akan sa ,
3. Akwai inda zaka iya bin mu ta email idan ka sanya email dinka ka danna “follow” to duk sanda muka sanya sabon posting za’a tura maka ta email din ka,
4. Sannan daga kan shafin idan ka ga abu yayi maka zaka iya danna alamar “share” ka tura shi zuwa Facebook, WhatsApp, Twitter da sauransu kai tsaye daga kan shafin
5. Sannan zaku iya bibiyar mu ta kafofin Facebook da Twitter ta yadda muna yin posting zaku dinga samun sa, zaku iya samun mu ta adreshi kamar haka:
-Facebook: www.facebook.com/agritech.com.ng
-Twitter: www.twitter.com/agritech_ng
-Instagram: www.instagram.com/agritech_nig

7. Zaku iya aiko mana da sanarwa ko tallace tallace da suka shafi noma da kiwo ta hanyar shafin www.m.me/agritech.com.ng
CEO Agribusiness Technology
01 January 2019
#Noma #Kiwo #Kasuwanci #Livestock #Poultry #Aquaculture #agritech.com.ng

About sharfadi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *