Yadda Fauziyya D. Sulaiman Ke ceton Rayuwar Al’umma Ta Facebook

Fauziyya D. Sulaiman fitacciyar mace mai amfani da shafukan sada zumunta na zamani wajen ceton rayukan al’umma marasa gata.

Wannan aikin da take yayi tasiri sosai hakan ke nuna cewa akwai gudummuwar da mata zasu iya bayarwa kenan a shafukan amman kuma har yanzu ana samun wadanda ke hana mata amfani da shafukan a duk sanda ka hana ‘yarka amfani da wadannan shafukan da zamani yazo dasu to ka sani zatayi amfani da wata hanyar daban, ko na kawaye ko kuma tayi badda kama.

A shekarun baya kadan na koyar a makarantar Islamiyya sau tari idan naga mace tayi min mgn Ina bincika sosai kafin na amince irin wannan nasha samun daliban mu amman sun canja suna a facebook saboda suna tsoron za’a hanasu, kaga ka jefata cikin halin rashin gaskiya.

Ba tsawaitawa zanyi ba tattaunawa ce nake son kawo muku wadda Nasir Abbas Babi na Garkuwa FM Sokoto yayi da Fauziyya D. Sulaiman ga kuma yadda tattaunawar ta kasance:

Fauziyya:
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.
Ni sunana Fauziyya D. Sulaiman an haifeni a shekara ta 1981 a karamar hukumar Fagge da ke Jihar Kano. Nataka matakin karatu daga Firamari harzuwa Babbar Diploma a school of hygiene Kano.
Nayi wasu Karin karatun a fannin computer, kiwon lafiya dakuma harkokin rubuce-rubuce.
Yanzu haka ina zaune da maigidana dakuma ‘ya’ya shida.
Wannan shine takaicaccen tarihina. Nagode.

Nasir Babi:
Me yaja hankalinki har kika fara anfani da shafin facebook?

Fauziyya:
Na fara anfani da kafar sadarwa ta facebook tun 2009/2010 saboda ganin kawaye ana tattaunawa. Ana cewa “muhadu a facebook” ko kuma “na tura miki sako ta facebook”. Wannan shiyasa nafara anafani da kafar sadarwa ta facebook.

Nasir Babi:
Me yaja hankalinki game da fara wannan mu’amala ta taimakawa marasa lafiya a shafinki na facebook?

Fauziyya:
Munfara harkar taimako a facebook lokacin da naga case din wani matashi dan shekara 22 “Fu’ad” a mahaifata Fagge. Yana fama da matsanancin ciwon koda, wadda takai anrasa kudin magani. Duk ‘yan uwansa sunyi iya bakin qoqari, gashi kuma ana masa wankin koda (dialysis) duka sati.
Antabbatar da cewa yaron hafizin AlQur’anine domin shi yake jan sallah a masallacin layinsu dama wasu masallatan. Wannan shine yat
tayarmun da hankali ganin cewa an rasa kudin da za’a cigaba da masa wankin koda har ciwon yayi tsanani. Duba da mabiya da nake dasu a shafin facebook, hakan yasa na dora hotonsa ko Allah zaisa asami taimako daga alumma. Don alokacin a fusace nake sai na bada sako atura, cewa “a Kano ga wani matashi mahaddacin Qur’ani yana fama da ciwo an rasa wanda zai dau nauyinsa.”
Saina sa account number na yaron da sauran bayanan da ake buqata. Cikin ikon Allah sai wannan sanarwar takai ga Mai Martaba Sarkin Kano. Hakan yasa muka tattara taimakon da muka samo, mukatafi wajen sarki. Sarkin yadau nauyin kula da lafiyar yaron har ya warke, da kuma shan alwashin cewa koda kuwa takai ga afitar dashi qasar waje.
Bayan sarkin Kano ya karbi ragamar kula da lafiyarsa, sai Allah yadau ran Fu’ad (RahimahuLLAH).

Daga wannan lokaci mutane suke mun magana da na taimaka musu ta hanyar rubutu a shafina. Sai nafiskanci cewa a matsayina na wacce take kamar ‘yar jarida, in mukai magana a shafin sadarwa mutane suna yadda, da kuma daukar abun da muhimmanci. Sai na cigaba da anfani da wannan damar wajen zaqulo mutane marasa lafiya. Da yake inada raunin zuciya, koya naga ciwo ina qoqarin na bada abunda nake dashi. Inkuma bazan iyaba, ina anfani da ilimina na hanyar kiwon lafiya domin har inada chemist (Shagon Magani) a shekarun baya. Harya kasance kullum magani na karewa a chemist din.
Har wani lokacin Maigida na yana mun fada dana daina biyewa mutane.

Duk mutumin damuka samu bashida lafiya, mukanyi posting, mukaishi asibiti. Bamu cika son abamu kudi ba, munfi son adau nauyi kamar yadda sarki yadau nauyin Fu’ad. Dakuma wani matashi “Murtala” wadda wata babbar qusa (mata), lamba ta daya a Nigeria ta dau nauyinsa. Da farko sarkin musulmi da sarkin Kano sun dau nauyin aikin (operation) da akaiwa Murtala nafarko, daga bisani ita (lamba daya a Nigeria) tadau nauyinsa gabadaya. Ganin cewa mutane sun anshi wannan aiki namu, sai muka dora, muka cigaba. Alhamdulillahi!

Nasir Babi:
Gashi kinada iyali, kuma kowa yasan cewa kina rubuce-rubuce, ga kuma aiki a Arewa24 wanda kuke wuni kuna rubutu na drama da sauran abubuwa. Tayaya kike hada wannan ayyuka dakuma taimakon marasa lafiya wanda basu da gata ta hanyar anfani da shafinki na facebook?

Fauziyya:
Maganar gaskiya hada wannan ayyuka abune mai wahala. Kamar yadda kafada aikin arewa24, aikine na NGO wanda in kafara tun 8 nasafe sai 5 nayamma. Sannan ga rubuce-rubucen film ga kuma wannan aikin (na taimakon marasa lafiya).
Ina shan wahala sosai domin har kasa bacci nake wani lokacin. A wasu lokutan sai nayi yunqurin haqura da maganar tallafin mutane, amma saboda raunin zuciyata da saurin kuka idan naga wani case din bansan sanda ma nake posting ba.
Ina samun masu tallafamin, insha Allahu muna qoqarin bude foundation dasu.

Sukan taimakamin wajen zuwa su dauko hoton mara lafiya, amma gaskiya nafi zuwa da kaina dan naga patient (Mara lafiya) na kaishi asibiti.

Munada wakilai ma’aikatan lafiya masuyi fisabililLAH a asibintin Murtala, Mallam Aminu, Orthopedic (Dala) da sauransu.
Nakan kirasu a waya natura musu patient (Mara lafiya). Abunda muka samu na donation (Tallafi) muna turawa mutane ta account.

Wani lokacin babu tallafin dazaka bawa mara lafiya, amma saboda tausayi na zuciya, kudadena dayawa suna shiga ciki.

Alhamdulillahi. Cikin ikon Allah wani lokacin tallafin da aka tara na mutum daya, yana isa muyi anfani dashi akan mutun biyu har zuwa uku.

Aikin yana shiga cikin ayyukana, yana kuma shiga cikin rayuwata. Amma damace da Allah yabamu. Innace zan bari sai nan gaba, bansan ko zan rayu har zuwa lokacinba. Hakan yasa nahaqura nacigaba.

Weekend dina yakan qare a ziyarar marasa lafiya, wanda zamuje mudau hotunansu da bidiyonsu. Akwai inda muke zuwa mota ma bata shiga, saidai mu ajiye motar mu taka da qafa. Wasu lokutan har goman dare ina kaiwa ina yawon bin gidajen marasa lafiya ina ganinsu. In mun sami case din da ba a Kano yake ba, sai mu tura wakilan da suke wasu Jihohin su taimaka mana.

*Fatanmu dai a kullum Allah ya amshi wannan aikin, ya kuma sanya a wanye lafiya.
Allah yayi sakayya da mafificin alkhairi.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
14-11-2018.
#HumanityFirst

About sharfadi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *